6 Yuni 2016 - 18:41
Abin da ya sa ba a yi wa Shaikh Zakzaky aikin idonsa ba - In ji Malam Badamasi Yaqoub

A ranar Talatar makon jiya ne, tawagar mutane 13 da ta kunshi iyali da ’yan uwa suka ziyarci Shaikh Ibraheem Zakzaky a inda ake tsare da shi. A cikin maziyartan har da babban dan Malam din, wato Sayyid Muhammad da Amaryarsa Malama Maimuna Ali Babba, inda ya yi masu addu’a da sanya albarka a auren da suka yi.

A ranar Talatar makon jiya ne, tawagar mutane 13 da ta kunshi iyali da ’yan uwa suka ziyarci Shaikh Ibraheem Zakzaky a inda ake tsare da shi. A cikin maziyartan har da babban dan Malam din, wato Sayyid Muhammad da Amaryarsa Malama Maimuna Ali Babba, inda ya yi masu addu’a da sanya albarka a auren da suka yi. Bayan sun dawo Aliyu Saleh ya tuntubi, Malam Badamasi Yaqoub don jin yadda wannan ziyarar ta kasance da kuma neman sanin dalilin da ya sa ba a yi wa Malam din aiki a idonsa ba a tsakiyar watan jiya, kamar yadda aka tsara tun da farko. Ga hirar.  

ALMIZAN: A makon jiya ne aka yi bikin babban dan Shaikh Ibraheem Zakzaky da kuka jagoranta, akwai abin da za ku bayyana ga jama’ar da suka halarta da kuma wadanda suka ba da gudummawa ta kowace fuska?

MALAM BADAMASI YAQOUB: Kwarai wannan biki abin farin ciki ne a gare mu, musamman da yake Allah ya nuna mana a cikin ’ya’yan tara, wato maza bakwai, mata biyu da Allah ya azurta Shaikh Ibraheem Zakzaky da su, daya ya yi aure. Da yake duk an karar da mazajen, sai wannan babban dan nasa ne ya rage, Muhammad. Shi ma sun rika fakon sa a lokuta daban-daban don su kashe shi, amma Allah bai ba su dama ba. Misali akwai wani lokaci da ya zo wucewa a NEPA a nan cikin Zariya, sai wani yake cewa ga shi nan wanda muke jira ya wuce. Ya ce muna so mu kashe shi ne don mu sanya wa Zakzaky bakin cikin da zai sa ya mutu. Wannan ta faru ne bayan waki’ar Kudus.

Amma tare da ikon Allah, bisa kariyar Allah ga Muhammadu, Allah ya kaddara ya yi aure. Wannan zuriya ta Alzakzaky da ba a so ta wanzu a doron kasa, muna rokon Allah ya wanzar da ita. Allah ya tabbatar da ita.

Gaskiya mun yi mamakin ganin yadda jama’a suka bumbunto ta ko’ina zuwa wajen wannan bikin, wasu Maulidin Shehu Ibrahim Nyass da aka yi a Katsina ya hana su isowa. Muna da labarin wadanda suka fito daga yankin Katsina, kusan kashi 70% ba su samu isowa wajen wannan daurin auren ba. Akwai wadanda suka kira ni suka shaida min. Shi ma Uban ’Ya, Alhaji Ali Babba ya fada min cewa akwai wadanda suka kira shi suka shaida masa haka.

Don haka gaskiya mun yi mamaki yadda jama’a suka bumbunto ta ko’ina duk da kuwa wadanda suka auka wa Malam Ibraheem sun yi haka ne don su raba shi da jama’a, amma kuma sai suka kara damfara shi da su. Lallai mun yi mamakin ganin Musulmi daga bangarori daban-daban, ba tare da bambancin fahimta ba, da kuma wadanda ba Musulmi ba, irin su Fasto Yohanna Buru duk sun halarta. Haka nan kuma zuwa wadanda muka jibincin dangantaka da su ta jini, lallai ya ba mu mamaki matuka. Tun daga wadanda muke Uwa daya Uba daya, zuwa wadanda muke Uba daya da su. Kusan za mu iya bugun kirji mu ce danginmu gaba daya na kauye sun zo. Mun jima ba mu ga bikin da ya tara danginmu gaba daya kamar wannan ba. Allah ya kara zumunci. Allah ya saka wa kowa da alheri. Muna fatan kowa ya koma gidansa lafiya. Allah ya gaggauta kwato mana Malam Ibraheem Zakzaky. Shi kuma aure da Muhammadu ya yi Allah ya albarkace shi, ya azurta su da ’ya’yan da za su maye gurbin wadanda aka rasa guda shida din nan.

ALMIZAN: Mun ji labarin shi Muhammad ya hadu da jarabawowi, an haife shi Mahaifinsa na tsare a kamun da Buhari ya yi masa a 1985, sai ga shi kuma ya yi aure, Mahaifinsa yana tsare a wani kamun da Buhari ya sake yi masa.

MALAM BADAMASI YAQOUB: Lallai wannan haka ne. Wannan abu ya bai wa kowa mamaki. A shekarar 1985 Janar Muhammadu Buhari ya kama Malam Ibraheem ya tsare shi a kurkukun Kirikiri, kuma ko a lokacin Buhari ya yi niyyar kashe Malam ne, kuma a lokacin ne aka haifi Muhammad. A lokacin Malam ya bar wasiyyar cewa in an haifi namiji ne a sanya Muhammad. In an samu mace ne ga abin da za a sa. Kuma yanzu ga shi Muhammad ya yi aure a lokacin da Buhari ya kama Malam.

A wannan karon ma an zo da nufin kashe shi ne, amma sai Allah ya nuna masu rai da mutuwa suna hannun Allah ne ba suna hannun wani ba ne. Duk luguden wutar da suka kwashe awa 48 suna yi, da jefa makamansu masu guba da bama-bamai da gurneti, Allah ya raya Malam. Yanzu duniya ta san Malam yana raye. Ba yadda za su yi da shi. Buhari ya tsare Malam a lokacin yana Soja, yanzu kuma ya kama shi yana Shugaban kasa na farar hula.

ALMIZAN: Bayan an kammala biki mun ji labarin kun ziyarci Shaikh Zakzaky, masu karatu za so su ji yaya ita wannan ziyarar ta kasance?

MALAM BADAMASI YAQOUB: Bayan an gama biki, mun tafi da Ango da Amarya da sauran dangi, mu 13 ne muka je, mata bakwai, maza shida muka ziyarci Malam din a wajen da ake tsare da shi. Malam ya albarkaci wannan auren, ya yi masu addu’a da nasiha daidai gwargwado.

ALMIZAN: Ko za a gutsaro mana nasihar da Malam ya yi masu?

MALAM BADAMASI YAQOUB: Nasihar da ya yi masu ita ce maganar hakuri. Ya ce shi aure dama dan hakuri ne. Ya ce, Hausawa suna da karin maganar da suke cewa, “zo mu zauna, zo mu saba.” Kuma suna cewa, “tsakanin harshe da hakori ma ana sabawa.” Ya ce, aure tamkar nau’i ne na zuma, in ka ji zakin sa yau, gobe zai iya zama madaci. Don haka aure dan hakuri ne. Idan daya ya taso, sai daya ya sauka. In kowa ya taso, sai ya zama ba za a fahimci juna ba. Daga baya kuma aka yi hotuna. Muna tare wajen awa hudu zuwa biyar.

ALMIZAN: Wannan karon kun je da yawa, za mu so mu ji wadanda aka je da su?

MALAM BADAMASI YAQOUB: To daga cikin wadanda muka je a wannan karon akwai ni, Muhammad, Amarya Maimuna, Mahaifinta, Alhaji Ali Babba, Kanwar Malam, Hajiya Maimuna, Malam Dalha, Malam Abdulrahaman Yola, Aminu Yabo, Nasifa Lawal, Yayar Malama Zeenat da kuma sauran ’yan uwa. Don haka za mu iya cewa an je ziyarar ne ta kowane janibi, da janibin shi Malam da kuma na Malama Zeenat da kuma ’yan uwa na Harka.

ALMIZAN: Da yake a wancan hirar da muka yi ka shaida mana cewa za a yi wa Malam aikin ido a farkon watan jiya. An samun yin aikin kuwa?

MALAM BADAMASI YAQOUB: Ba a samu yin aikin ba. Amma shi Malam din ne da kansa ya nemi a dage aikin zuwa wani lokaci, saboda ya ce idan an tafi wannan aikin zai yi asarar ayyukan da ake yi na Nisfu Sha’aban, saboda haka sai ya ga cewa da ya yi asarar ayyukan Nisfu Sha’aban din, gwamma a dage aikin zuwa wani lokaci nan gaba.   

ALMIZAN: To ya yanayin jikin Malam din?

MALAM BADAMASI YAQOUB: Kamar yadda na sha fada, gaskiyar magana jikin Malam ya yi sauki sosai. Duk ayyukan da aka yi masa an yi nasara, sai dai mun lura akwai dan saura a hannunsa na hagu saboda har yanzu yatsunsa na hagu ba sa tankwaruwa sosai, kuma yana gaya min cewa in ya sa ruwan sanyi yana jin wani abu, don haka ba ya amfani da ruwan sanyi, yana amfani da ruwan zafi ne. Ta janibin fuska kuma, kamar yadda na fada maka a waccan hirar da muka yi, idanuwansa biyu duk an harbe su, kuma na hagu ya yi muni, don sai da ya zazzago ya fito, shi Malam din ne da kansa ya dauki idon ya koma da shi, shi da ka gan shi babu wata tambaya, ka san yana da matsala. Shi ma na daman yana da matsala, domin an yi ciko ne a ciki, mutum ba zai ga cikon ba, shi kuma na hagu za a yane yanar da ke ciki ne.

ALMIZAN: Ko akwai wani sako da Shaikh Zakzakya ya bayar ga ’yan uwa?

MALAM BADAMASI YAQOUB: Sakon da ya bar ga ’yan uwa a wannan karon bai bambanta ba da wanda ya bayar a wancan zuwan da muka yi ba. Ya ce, duk wani abu da aka sani Harka kar a fasa, sawa’un Ta’alimomi ne, Muzaharori ne, munasabobi ne, a ci gaba da gudanar da su kamar Malam yana nan. Sai kuma ya sake jadadda mana cewa lallai mutanen nan da ya saba bai wa kayan Azumi, a ba su, kar a fasa.

ALMIZAN: Daga karshe akwai wani kira da kake da shi ga ’yan uwa?

MALAM BADAMASI YAQOUB: Kiranmu ga ’yan uwa shi ne, wannan abin da Malam ya fada na a ci gaba da gudanar abubuwan da aka saba yi na Harka, lallai a ci gaba din, tamkar Malam din yana cikin mu. A ci gaba da gudanar da wadannan program din cikin hadin kai da fahimtar juna. Ina kira ga ’yan uwa kar su rarraba, kar su ga cewa tunda Malam ba ya nan ba za su yi abu kaza ba, ko kuma su ji cewa yanzu babu Jagora, ko babu jagoranci. A Harkar nan kowane lokaci akwai jagoranci. Alhamdullahi Malam yana nan da rai. A baya idan Malam ba ya nan ko an kama shi, Malam Muhammad Turi ne ke jibintar lamuran ’yan uwa, shi kuwa ga shi Allah ya kaddara ya yi shahada a wannan harin da suka kawo. Yanzu jibintar al’amarin ’yan uwa yana wuyan Malam Yakubu Yahya ne, muna fatan duk abin da za a yi ya zama umurnin yana fitowa ne ta hannun Malam Yakubu Yahya.

Kamar yadda na fada a waccan hirar da muka yi, a wannan karon ma zan sake jadaddawa, ’yan uwa su tuna muna da makiya na ciki da waje, don haka kar mu yarda wata baraka ta taso a tsakanin mu, ko kuma a yi amfani da wasu, su wuce gona da iri, wannan zai zama ya biya bukatar makiya ne. Kar mu manta ba wai sun hakura ba ne, har yanzu suna neman hanyoyin da za su bi ne wajen sake auka wa wannan Harkar, tunda har yanzu bukatarsu ba ta biya ba. Mun ga abin da suka yi a Katsina na kai sojoji da nufin auka wa jama’a. Muna ganin take-takensu a Jos, wanda suke da niyyar rusa Markaz. Wadannan nan duk wasu matakai ne na tsokana, wanda suke so su tunzura ’yan uwa su dauki wani mataki da bai dace ba. Saboda haka lokacin da makiyinka ya zama mahaukaci a kanka, ya kamata kai kuma ka zama mai hankali a kansa. Mu yi amfani da hankali da ilimin da aka san mu da shi.

Kowa ya san abin da ya faru a Zariya, sun yi amfani da hauka ne, sai aka yi masu amfani da hankali, sai ga shi sun rasa yadda za su yi. Kamar yadda Malam yake cewa mu ke da ilimi, su ko ba su shi. Mu ke da hankali, su ba su da shi. Ina fatan ’yan uwa za su rika amfani da ilimi da hankali a duk lamurransu.

Ina so in yi amfani da wannan damar wajen yin kira ga jama’ar da suke ganin su ba ’yan Shi’a ba ne, don haka babu ruwansu da abin da aka yi mana. Yana da kyau su fahimci cewa matsawar kuna zaune a kasa daya, duk abin ya shafi wani, kai ma zai iya shafar ka, sawa’un Musulmi ne ko Kirista, matsawar mutum ne bil’adama. Annabi (S) yana cewa Musulmi da Musulmi tamkar gini guda ne, sashe ne ke karfafa sashe, in bangare guda ya rushe, daya ma zai samu matsala. A wani lokaci kuma ya siffata su da jiki guda, cewa idan bangaren jikinka yana ciwo, kamar karamin dan yatsa, duk sauran jikin kan dauka. Don haka ya nuna al’ummar Musulmi abu daya ne.

Ya kamata al’ummar Musulmi su gane cewa in an dirar ma wadansu, gobe za a iya dirar masu. Ballanta ma ba a taba dirar wa wani mutum ba, ya zama bai shafi wani ba, wannan harin da aka kawo mana ya shafi mutane da yawa, ciki har da Student da Almajirai da mutanen gari. Haka shi ma Kudus da aka yi ya shafi mutane da dama har da ma’aikatan Banki.288